Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi wa sallam yace "wani musulmi bai kasance ba yana rokon Allah da wata addu'a wadda ba sabawa Allah a cikinta ko kuma yanke zumunci face Allah ya bashi dayan ukun nan: ko dai Allah ya gaggauta karban addu'an sa, ko kuma Allah ya ajiye masa ladan abin da ya rokan ya zuwa ranar lahira, ko kuma ya tunkude masa wata cuta kwatankwacin ta. Sai suka ce: mu yawaita kenan? Sai manzon Allah yace, Allah ne mai bayar da mafi yawa. Imamu Ahmad da turmizi.
'Yan uwa abokaina mu dage da addu'a, Allah zai amsa mana, musamman halin da muka tsinci kanmu a wannan kasa tamu mai albarka, mu dage, Allah yana son naci, mu nace mu nace mu nace, Allah ya datar damu alkhairin sa.
No comments:
Post a Comment