ALAMOMIN SON ANNABI (S.A.W.).
Dukkanin yabo da godiya sun tabbata ga Allah maɗaukakin sarki mai kowa mai komai.Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabin rahama wanda Allah ya aiko shi don ya zama rahama ga halittu baki ɗaya, da iyalan gidan sa da sahabbansa da waɗanda suka biyo bayan su da kyautatawa har izuwa ranar sakamako.
Ba bu shakka son Annabi{tsira da amincin Allah su tabbata agare shi}iba ne,kuma addini ne idan aka ce so ko ƙauna,abinda ake nufi da ƙauna shi ne ratayuwar zukata da karkatarsu zuwa ga abin da su ka yarda da shi ko su ke tunanin kyakkyawa ne zuciyar ɗan'adam ta karkata ko ta rataya a bisa ƙauna ko soyayya .Soyayya ko ƙauna ta na kasuwa zuwa kashi uku:
*Kashi na farko shine kaso abu sabo da ɗan ɗanonsa ko daɗin sa,kamar yadda ɗan adam yake son wani nau'i na abincin ko nau'i na abinsha wanda ya ke jin daɗin sa ko ɗan ɗanon sa da harshen sa, haka kuma ko ɗan adam ya so mace sabo da tana ɗauke ma sa kewa wannan shine kashi na farko na soyayya ko ƙauna.
*Kashi na biyu na ƙauna ko soyayya shine son abu don amfanin sa don ɗan adam yan amfanuwa dashi,kamar yadda ɗan adam yake son gidan da ya ke zaune, matsugunin sa abin hawan sa doki,raƙumi ,alfadari,mota, mashin da dukkan kayan sufurin da ɗan adam yake amfani da shi.Wannan ɗan adam yana san su sabo da yan amfanuwa da shi.
*Sannan abu na uku ɗan adam yana san wani abu don falalar sa, da matsayin sa, da ƙimar sa kamar yadda ake son bayin Allah nagari, Annabawa, Manzanni da sauran mutanen kirki da ake ƙaunatar su,wannan shine kashin ƙauna guda uku.Ko da ban faɗaba kun san cewa son da akewa Manzon Allah{tsira da amincin Allah su tabbata agare shi},zai shiga cikin kashi na ukun nan na so ko ƙauna, ba wai don ɗan ɗanon sa ba, a'a ana son Manzon Allah{tsira da amincin Allah su ƙara tabbata agare shi} sabo da falalar sa, sabo da darajar sa, sabo da ƙimar sa.
Zamu iya kasa alamomin Manzon Allah{tsira da amincin Allah su ƙara tabbata agare shi}, manya daga ciki zuwa kashi bakwai.
{1} Kashi na farko ana son Annabi{tsira da amincin Allah su ƙara tabbata agare shi} saboda ana amfanuwa dashi domin bin sa shine tsira, yin imani da shi shine lasisin shiga al-janna ranar al-ƙiyama, wannan shine kashi na farko na so ko ƙauna.
{2}Abu na biyu son Annabi {tsira da amincin Allah suƙara tabbata agare shi}wajibi ne tilas ne, dalilai na Al-ƙur'ani da Hadisai sun bayyana haka daga, daga cikin ayoyin da ake kafa hujja dasu waɗanda suke nuna wajabcin son Manzo Allah{tsira da amincin Allah su ƙara tabbata agare shi} shahararriyar ayar nan da take cikin suratul {TAUBA 9:24}'' '' wannan aya ta jeranta dangin abu buwan ƙauna guda takwas wanda a'al'adance ɗan adam yana san su daga ciki nafarko a kwai 'ya 'ya, nabiyu akwai iyaye daga ciki uku akwai 'yan'uwa, yayye ko ƙanne maza ko mata,sannan na huɗu akwai mace,sannan na biyar akwai dangi sawa'un dangin uwa ko dangi na ɓangaren uba,sannan na shida dukiya da ɗan adam yake mallaka, sai na bakwai wata hada-hada ta kasuwanci wadda ɗan adam yake cin moriyarta, daganan sai na takwas shi ne gida da ɗan'adam yake zaune acikin sa, matsuguni ko mahalli.Ubangiji ta'ala yace''Idan waɗannan al'amura guda takwas suka zama mafi soyuwa agurinku su ku ka fi ƙauna, kunfi son su sama da ƙaunar Allah sama da ƙaunar Annabi{tsira da amincin Allah su ƙara tabbata agareshi},kunfi son su sama da yadda kake son gwagwarmaya dan yaɗa kalmar Allah aban ƙasa.Idan haka ne to ku jira''wannan lafazi yagunshi razani da firgici.Ma'ana kuso su ɗin kwaga abinda zai biyo baya, kafifita su ɗin akan Allah da Manzon sa da Jahadi wajen ɗauka ka addinin Allah aban ƙasa kuyi hakan ''Har yazuwa lokacin da Allah zaizo da al'amarinsa, Ubangiji ta'ala baya shiryar da mutanen da suke fasiƙai.''Alƙali iyal cikin littafin sa AL'SHIFFA BIL TARIFIL HULƘATUL MUSTAFAH yace ''wannan aya ko shakka ba bu ta ƙunshi zaburarwa da janhankali, da zuga mutane da zaburarda su kan suso manzon Allah {tsira da amincin Allah su tabbata agare shi} sama da ko wa aban ƙasa, sannan kuma ta shafi jan kunne da nu ni zuwa ga cewa son annabi{tsira da amincin Allah sutabbata agare shi} abune wanda yake wajibi.Domin Ubangiji subuhanahu wata'ala ya ƙwan ƙwashi zukatun mutane cewa idan son 'ya'yan ku da iyayen ku da danginku shine a'ala da aula awajen ku to ubangiji ya yi muku razani. Sannan ubangiji ta'ala ya mai shesu fasiƙai da yace da ɗai ubangiji ta'ala baya shiryar da mutanen da suke fasiƙai.''
Imam Bukhari da Iman Musulum sun rawaito hadith da ga abu Huraira Allah yaƙara yarda agare shi,manzon Allah {tsira da amincin Allah su tabbata agare shi yake cewa''Narantse da wanda raina yake hannunsa ɗayan ku ba zai zamo mai imani ba har sai na zamto abin so awajen sa sama da yadda yake son 'ya'yan sa''wannan hadisi aruwayar Bukhari shi kaɗai, amma aruwayar dayake imam Muslim yayi tarayya da imam bukari awajen ruwaya, ankarbo daga anas dan malik Manzon Allah (SAW) yake cewa ''Layumin ahadakum hatta akunu ahabba ilaikum hatta akunu ahabba ilaikum min walidihi wa waladihi wannasu ajama'i''ma'ana ''Dayanku ba zai zamo mai imani ba har sai na zamo abinso awajensa sama da dukkan mutanen duniya gaba daya.''Wannan nassi sunna nuna wajabcin kaunar Manzon Allah(SAW).Kuma kasancewar Manzon Allah(SAW) kaunar sa tazama dole ma'ana wani abu ne da za'afada don amai-mai ta, amma duniya bata taba yin wani mutum ba ada ko ayanzu ko alokacin da zaizo nan gaba wan da jama'a suka y ittifaki son sa irin Manzon Allah(SAW) ka kaf musulmi suna kaunarsa sannan wasu daga cikin kafirai suna sonsa.Dukkan mumini mace ko namiji yana ganin girman sa sannan wadansu daga cikin kafirai yahudu ko nasara ko mushurikan makka sunyi masa jin jina cewa shi bardai ne jarumi wanda duniya bata taba ganin irinsa ba rana bata taba haska kan wani me daraja irinsa ba(SAW). Gabar magana ta uku meke sa aso Annabi (SAW) wanda ake kira da''wa,il muhabba''domin idan kaga kaso abu akai abin da yasa ka ke sonsa, idan ba dalili bazaka soshi ba.Bayadda zaka ce ina son wane kawai don shi wane ne batare da wani dalili ba da yasa kake son sa ba dole akwai wani dalili, jaruntar sa kyan halittar sa kyan dabi arsa, kyan halin sa, kyautar sa ko wani abu ma kaman cin haka ko kuma an wajabta ma kaso shi ko da bai taba yi ma ka bajin ta agaban idon ka kaganiba, ko da bakaci moriyar kyautar sa ba da yalwar hannu dayake dashi ba wannan shi ne wa'il mu habba. Farko daya daga cikin ababan dake sawa akaunaci Annanabi(SAW),dukkan musulmai suna san Allah to son Allah baya cika sai ka so Manzon Allah(SAW).Idan da zaka kaunaci Allah kaxai ka ta qaita akan kaunar sa ba tare da ka qaunaci Manzon sa ba to son da kake wa Allah ya zama naka sasshe kuma ba zai maka amfani ba, ba zai tserar da kai ba daga huta kuma bazai yi sana diyar ka shiga Al-jannah ba.Ashe kaga anan dolene kaso Annabi ta wannan fuskar don haka Allah yace '' .'' Al-imam Ibn Kasir yace wannan ayar kamar wata kotuce da takewa mutane hukunci dukkan wanda yayi da'awar son Allah sai aduba aiyukan sa da maganganunsa idan yana tafiyar darayuwar sa irinta Manzon Allah(SAW), yana kokarin kwai kwayon sa cikin maganganu da ayyukansa to son da yake wa Allah gaskiyane.Amma sai aka duba aiyukan sa da magan ganun sa ba koyi da Manzon Allah(SAW) to son da yace yana yiwa Allah ba gaske bane don ayar tace '' .'' Idan dagaskene kunason Allah to kubi Manzon Allah (SAW).Idan bakabi Manzon Allah ba to karyane da'awar da kayi, kamar yadda Hasanul Basari yake cewa ''Ayar jarrabawa take bayarwa.
Sannan abu na biyu shi Manzon Allah (SAW) zabine na Allah, Ubangiji ta'ala yazabe shi ya fifita shi akan kowa.Hadisi ya tabbata acikin sahihul muslim daga Wasi'a ibn Asqan (RA) yace da kaina naji Manzon Allah yana cewa ''ka kaf daga cikin zuriyar gidan Annabi Isma'il, sai Allah ya zabi Kinana yafifita dangin gidan Kinana sukafi sauran falala idan aka kwatanta da sauran zuriyar gidan annabi Isma'il. Daga cikin 'ya 'yan kinana sai Allah yazabi Qurash-shawa wadanda su suke dangan tuwa zuwa ga Qurash su sukafi sauran daraja,daga cikin qurasshawa sai Allah ya zabo banu Hashim, sunfi sau ran gama garin kurasshawa,daga cikin banu hashim ne sai Allah yazabo Manzon Allah, don haka zavavvan zavavvu ne sai da aka tace aka rai raye aka tankaxe sannan aka ciro shi (SAW). To kaga shi zabine na Allah, kamar yadda yace acikin hadisin ruwayar Bukhari da Muslum ya ce ''Misalina da sauran annabawa kamar magini ne da ya gina wani qasaitaccen gida ya kammala komai acikin sa sai wani waje da bulo xaya kawai za'asa gidan yacika sai aka kyale gidan ba'asanya wannan buloba awani vangare da ga van garori nagidan, ga gida ya kai gida amma gawata qofa da ba'atoshe ba, ba'acike taba mutane duk wanda ya zaga yaga gidan zai ce ga gida ya kai gida sai dai kash inama ancike wannan wajen, ansa bulo xayan da gida ya gama cika, sai manzon Allah (SAW) yace Ni ne cikon bulo xin, ni ne cika makin Annabawa. Daga shine aka to she qofar annabta aka garmaqe qofar manzanci. Shine na qarshen su amma shine mafificin su kuma shi ne shugaban su jagoran su (SAW) wannan hadisin Imam Bukhari da Imam Muslum sukai tarayya wajen rawaitoshi.
Awani hadisin daban wanda Imam Bukhari ya rawaito daga Abu Huraira (RA), Manzon Allah (SAW) ya ce ''Allah maxau kakin sarki idan yaso wani cikin mutane sai ya kiraho mala'ika Jibirilu yace dashi Ina son wane! Kaso shi sai mala'ika Jibril yaso wannan mutum, sannan sai mala'ika Jibril ya yi shela asama duk ba wani mala'ika face sai yaji shelar sa, ya na cewa Ubangiji (SWA) yana son wane ku so shi, duk mala'iku dake sama sai su so wannan mutum, sai asa masa karvuwa awajen sauran mutane na qasa. Wato da Allah yaso Annabi (SAW) sai yagayawa mala'ika Jibril, sai mala'ika Jibril yabada shela dukkan mala'iku suka kaunaci manzon Allah (SAW) kaga mala'iku suna da yawa bawan da ya san adadin mala'iku sai dai Allah sannan kuma sai akasa masa karvuwa aban qasa. Karvuwa baga mutanan da sukai zamani dashi ba kaxai, mutanan da suka zo kafin zuwan sa, sun ji labarin zai zo an bada busharar zuwan sa acikin littattafan su, da kuma muganan da sukai sa'ar tozali, da kuma mutanan da zasu zo bayan sa har izuwa ranar tashin al-qiyama. Bawanda yatava samun masoya irin sa (SAW), don haka kaga wannan zavine na Allah, da Allah yazave shi sai ya zamto jama'a suna qaunar sa ta wannan fuskar.
Abu nagaba daga cikin dalilan da ko sbuban da ke sawa aso Manzon Allah (SAW), tausayin sa ga al'ummar sa axabi'a mutane na son mai tausayi, basason mara tausayi. Duk shugaban da yake tausayin al'ummar sa, sai kaga jama'a suna qaunar sa, duk shugaban da baya tausayawa al'ummar sai kaga jama'a basa son sa, basa qaunar sa. To manzon Allah acikin dukkannin shuwagabanni da aka tava yi aduniya ba mai tausayi irin nasa, ba kuma mai jinqai irin nasa(SAW), don haka Allah yace ''Allah ya turo shi don yazama rahama gamutane gaba xaya. Malamai sukace muminai dama kafurai duk manzon Allah rahama ne agare su, sai dai ajikin muminai ta bayyana domin sunyi imani da shi zasuci moriyar imanin anan duniya da gobe qiyama, anan duniya imanin yatsare musu jinin su, ya tsare musu dukiyoyin su ta yadda ba za a yaqe suba aribace dukiyar su amatsayin ganima, alahira kuma imani yazama garkuwa daga shiga huta.
Kafurai kuwa da basuyi imani da shi ba, suma sun ci moriyar zuwan manzon Allah domin dayazo yakira su dasuyi imani sukaqi sai ya yaqesu aka karkashe su, kisan da aka yi musu amfani zaiyi musu domin daya qyale su duk minti xayan da zasu qara to suna qara yawan laifi ne akan su da aka kashe su sai mala'iku suka huta da rubutun zunubi sai na da dasuka yi kafin akashe su, za'a kama su da shi ranar tashin al-qiyama, da an qyale su ba akashe su ba'a kashe su ba da ba a yimusu gata ba. Don haka kisan da Manzon Allah (SAW) ya yi musu afilin yaqin Badar da Uhdu da sauran ya qoqin da ya yi, gata yayi musu don arage musu azaba, ma'ana ya kasance aiyukan su na zunubi ya taqaita domin yawan zunubin da aka aikata yawan azaba. Yawan zunubin da aka aikata yawan azabar da za a fuskanta aranar alqiyama, don haka zuwan Manzon Allah (SAW) rahamace ga al'umma, me tausayi yake (SAW).
Imam Bukhari da muslum sun rawaito hadisi, lafazin na imam Muslum ne Manzon Allah (SAW) yace''kowanne annabi Allah ya yi masa alqawarin roqi in ba ka duk annabawa kowa sai yaroqi Allah anan duniya aka bashi yace nikuma tawa sai na boye ta nace abari sai alahira akace to me ka ke so a lahira sai nace so nake alahira abani damar ceton dukkan wanda yamutu bai tava shirkaba acikin al-ummata.'' Ceton nan na Annabi (SAW) zai shafi duk wanda ya mutu baya shirka baya bautar kabari baya bautar lata da uzza, baya bautar wanin Allah wato tsantsar ahalul sunnah ke nan wannan shine wanda zai dace da ceton Annabi (SAW), ka ga wannan tausayin Annabi ne(SAW) yasa ya ajjiye wa al'ummar sa wannan ceton sai alahira, Allah yasa Mu Dace
2 comments:
Godiyamuke
HATTARA MUTANEN AREWA
'YAN MATA SAMA DA 40 SUN YI
JIGIDA DA NAKIYOYI SUN SA
HIJAB SUN SHIGA BARNO.
Akwai maza da Ke bin mu a
baya da remote suke tada
Bom din da akai mana wiring
in mun isa wurin da aka tura
mu.
(Inji wata yarinya da civilian
Jtf suka kama)
Mun kama bakwai cikin su
muna neman sauran.
ANA NEMAN WATA MOTA
DAUKE DA 'YAN MATA ASHIRIN
MAI FENTIN SOJAN SAMA
Mun tsaida su basu tsaya ba
Mun bisu a baya sun bace
mana.
(Inji MUHAMMAD GAVA
commander civilians JTF a
Maiduguri.)
Wata majiya ta sirri ta ce
wannan wani sabon shiri ne
da CAN ta shirya don
hukumomin tsaro su haramta
wa matan musulmi sa hijabi a
Najeriya.
Majiyar tace kiristocin najeriya
na cike da haushin Janar
Babangida don me zai yi wa
Najeriya rijista da OIC Kasar
da rabi da rabi kirasta ne
Amman yanzu duniya na
kallon Najeriya a matsayin
kasar musulmi.
Post a Comment